Kungiyar Hizbullah ta fitar da wani bayani a jiya Talata da ta yi Allawadai da takuhkumin da kasar Australia ta kakaba wa babban sakatarenta Sheikh Na’im Kassim.
Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kunshi cewa; Matakin, yana sake nuni ne da hakikanin fuskar wannan kasa da a kowace rana take tabbatar da cewa, ita makami a hannun Amurka da Isra’ila.
Hizbullah ta kuma bayyana matakin da cewa na zalunci ne wanda bai jingina da kowane irin dalili na shari’a da halayyar kwarai ba, yana nuni ne kai tsaye da cewa; Suna goyon bayan HKI ne da kuma kare laifukan da take tafkawa da ta’addancinta, tare da yin kira cewa kamata a yi ace kasar ta Australia da ta dauki matakai ne na ladabtarwa akan ‘yan sahayoniya makasa, ta kuma kasance a tare da wadanda ake zalunta a Lebanon da Falasdinu.
Bayanin ya kuma ce: Duk duniya ta ga yadda abokan gaba ‘yan sahayoniya su ka rika yin kisan kiyashi da laifukan yaki akan wadanda ba su ji ba su gani ba a Gaza da kuma Lebanon, don haka duniyar ta san wanene dan ta’adda na hakika, da kuma wanda yake yin kisan kiyashi da tafka laifukan yaki.
Haka nan kuma bayanin ya ce, duniya ta kuma san su wanene suke bayar da kariya ga ‘yan mamaya a siyasance, yake kuma yin tarayya da ita a kisan kiyashin da take yi.
Sai dai kungiyar ta Hizbullah ta ce, wannan matakin babu yadda zai yi tasiri akan ‘yan gwgawarmaya a cikin Lebanon, ko kuma akan matakan da Hzibullah take dauka na kare kasa da al’umma da kuma kasancewa a tare da al’ummar Falasdinu.