Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun bada sanarwan kai hare hare kan wurare da dama a yankunan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Almamis.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani bayanin da dakarun kungiyar suka fitar wanda yake cewa, mayakan kungiyar sun kai hare hare da makamai masu linzami samfurin Katyusha kan sansanin sojojin HKI a garin Manot Moshay dake yammacin yankin Galilee inda suka wargaza garkuwan makamai masu linzami na sojojin kasar da dama.
Labarin ya kara da cewa makaman hizbullah sun fada da kan sansanin sojojin Artilary na HKI a yankin. Haka nan makaman na hizbullah sun fada kan barikin Zarit wanda shi ne cibiyar sojojin HK a arewacin kasar wanda suke kira ‘western Battalion’.
Hizbullah ta kara da cewa ta yi amfani da makamai masu linzami da ake kira Burkan kan wurare da dama a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye kuma sun haddasa barna mai yawa ga yahudawa.
Daga karshen kungiyar ta bayyana cewa ta kai wadan nan haren hare ne don maida martini kan hare haren da jiragen yakin HKI da kuma wasu makamansu suka kai a kan garuruwan kudancin kasar Lebanon.