Kafofin yada labaran da suke kusa da kungiyar Hizbullahi sun watsa labarin sakon da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta aikewa jagororin haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Ba za su iya kwato yankunan matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke arewacin Isra’ila da mayakan kungiyar Hizbullahi suka kwace ba.
Sakon kungiyar ta Hizbullahi ya jaddada cewa: Yadda karfin gwagwarmayar ya yi nasarar kwato yankunan ta hanyar tsananta kai munanan hare-hare a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, to ba zai yiwu cikin sauki a kwace daga hannun ‘yan gwagwarmaya ba.
Har ila yau kungiyar ta watsa wani tsohon sauti na shahidin gwagwarmaya Sayyid Hassan Nasrallah, da ke cewa: ‘Yan sahayoniyya ba za su iya kwato matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suka mamaye da karfi da suke arewaci ba, bayan da ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi suna ‘yantar da yankunan da karfin makamai.