Hizbullah Ta Bukaci Shugaban Cocin Katolika Na Duniya Yayi Tir Da Hare-haren Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullah ta kasar Labanon ta yi kira ga shugaban cocin katolika na duniya pope leo na 14 da zai kai

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar hizbullah ta kasar Labanon ta yi kira ga shugaban cocin katolika na duniya pope leo na 14 da zai kai ziyara kasar labanon da yayi tir da hare hare da rashin adalcin da isra’ila ke yi kan kasar labanon duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a shekarar bara.

Wannan sanarwar ta zo ne adaidai lokacin da shugaban cocin katoli na duniaya Pope Leo na 14 zai kai ziyara kasar labanon a wannan makon inda ake sa ran zai gana da kungiyoyin farar hula da kungiyoyin addini, inda zai ziyarci masallatai da majami’u, da yin adduoi a gabar tekun Beirut domin tunawa ga wadanda hari 2020 ya shafa, kana kuma yayi ganawa ta musamman da shugaban kasar Joseph Aoun.

Idan ana iya tunawa a cikin bayanan da babban sakatare janar din kungiyar hizbullah yayi a ranar juma’a shaikh Naim Qasem yayi maraba da ziyarar da pope Leo na 14 zai kai kasar ta labanon, kuma yace mambobin kungiyar za su mika masa wata wasika wadda za’a yadata ga kowa ta kafafen yada labarai

Tun daga lokacin da aka kulla yarjejeniyar dakatar da bude wuta isra’ila ya keta yarjejeniyar fiye da shurin masaki, na kai hare-hare kan kasar labanon duk da gargadi da gwamnatin kasar tayi mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments