Hizbullah: HKI Zata Yi Asara Mai Yawa Idan Ta Game Kasar Lebanon Da Yaki

Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wacce take fafatwa da sojojin HKI a kan iyakokin kasashen biyu, Sheikh Na’im Kasim ya bayyana cewa, kungiyarsa

Mataimakin shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, wacce take fafatwa da sojojin HKI a kan iyakokin kasashen biyu, Sheikh Na’im Kasim ya bayyana cewa, kungiyarsa bata neman yaki, amma idan HKI ta dora mata, to kuwa zata kare kasar Lebanon da duk karfinta.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya Asabar a wani jawabinn da ya gabatar a birnin Beirut babban birnin kasar. Ya kura da cewa dakarun kungiyarsa suna fafatawa da sojojin HKI tun ranar 8 ga watan Octoban da ya gabata, saboda tallafawa falasdiwa a Gaza da kuma maida martani kan hare haren da sojojin HKI suke kaiwa a ko wace rana a kudancin kasar Lebanon.

Wasu kakafen yada labarai sun bayyana cewa hare haren Hizbullah a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye ya yi sanadiyar halakar yahudawa kimani 50 mafi yawansu sojoji.

Sannan kungiyar ta kai hare hare kan wurare masu muhimmanci a cikin HKI wadanda suka hada da Bangaren da ake kira ‘Unit 8,200’ na babar ciyar leken asiri na HKI a cikin watan Augustan da ya gabata, tare da amfani da makaman linzami samfurin katsusha.

Banda haka ta tilastawa yahudawa fiye da 200,000 kauracewa yankin arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma ta rufe dukkan harkokin kasuwanci da yawon shakatawa wanda yankin ya shahara da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments