Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine.
Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana a wannan Talata a yayin wani taron manema labarai cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”.
Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.”
Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki kimanin sa’a daya kuma zai hada da jawabin babban sakataren kungiyar Sheikh Naim Qassem.
Sayyid Nasrallah ya yi shahada ne a yayin harin bam da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Beirut a ranar 27 ga Satumba, 2024.
Shi kuwa Safieddine ya yi shahada a lokacin harin da Isra’ila ta kai a watan Oktoban 2024.
Kungiyar Hizbullah ta dage bikin jana’izar shugabannin biyu saboda fargabar hare-haren Isra’ila a yayin bikin.