Hezbollah, Ta kai Hare-haren Rokoki Kan garin  Safed

Kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan garin Safed da ke arewacin Isra’ila a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa. “Don kare

Kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan garin Safed da ke arewacin Isra’ila a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.

“Don kare Lebanon da al’ummarta” da kuma ” mayar da martani” ga “hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kai kan garuruwa, kauyuka da fararen hula”, mayakan Hezbollah sun kai hari kan “Birnin Safed” da “rokoki 80”, inji kungiyar a cikin sanarwar manema labarai.

A halin da ake ciki dai Faransa da Amurka na jagorantar wani yunkurin tabbatar da an tsagaita wuta na kwana ashirin da daya cikin gaggawa a kudancin Lebanon.

Shugaba Macron ya ce tsagaita wutar na wucin gadi zai bada damar amfani da diflomasiyya wurin warware rikicin da ke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbollah.

Ya ce bai kamata a yi yaki a Lebanon ba. “Shi ya sa muke kira ga Isra’ila da ta dakatar da ayyukan da take gudanarwa a Labanon, ita kuma Hezbollah ta daina harba makamai masu linzami cikin Isra’ila.”

Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya ya ce Isra’ila ba ta son barkewar yaki amma ba za ta nade hannu ta ki yin komai ba bayan da aka kai wa yankinta na arewa hari.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya umurci sojojin Isra’ila da su ci gaba da luguden wuta kan wuraren ‘yan kungiyar Hezbollah a Lebanon, duk da kiraye-kirayen tsagaita wuta da ake yi.

Ministan harkokin wajen Isra’ila ya ce ba za a tsagaita wuta ba, har sai an samu nasara a kan Hezbollah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments