Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane 970 cikin sa’o’i 48.
Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kaddamar a ranar Talata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 970.
Wasu rahotanni na daban ce mutane 356 ne suka mutu a harin da aka kai ta sama, a cikin sa’a huda sannan akalla Falasdinawa 1,000 ne suka samu raunuka.
Wani babban jami’in Hamas ya shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa hare-haren na Isra’ila na nufin cewa Isra’ila ta kawo karshen tsagaita bude wuta a Gaza da aka fara a ranar 19 ga watan Janairu.
Mohammed Zaqout, babban darektan asibitocin Gaza, ya yi kira ga kasashen duniya da su shiga tsakani tare da tilastawa Isra’ila ba da damar samar da magunguna a cikin yankin.
Mata da yara da dama na daga cikin wadanda aka kashe
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce akalla Falasdinawa 61,700 ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da jikkata 112,041 a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.