Hare-haren Isra’ila Sun Yi Ajalin ‘Yan Gudun Hijira 35 A Rafah

Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kasha gomman ‘yan gudun hijira a sansaninsu dake kusa da binrin Rafah. A cewar hukumomin Hamas, a zirin

Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kasha gomman ‘yan gudun hijira a sansaninsu dake kusa da binrin Rafah.

A cewar hukumomin Hamas, a zirin Gaza, akalla mutane 35 ne suka rasa rayukansu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wannan harin na Isra’ila.

Fadar shugaban Falasdinu da kungiyar Hamas sun ce Isra’ila da aikata “kisan kiyashi” ta hanyar kai hari kan wata cibiyar ‘yan gudun hijira da ke kusa da Rafah, a kudancin zirin Gaza.

“Wannan kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi, ya saba wa dukkan kudurorin kasa da kasa,” in ji fadar shugaban Falasdinawa a cikin wata sanarwa, inda ta zargi Isra’ila da “kai hari da gangan” sansanin ‘yan gudun hijira na Barkat, wanda hukumar MDD ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu a arewa maso yammacin Rafah.

Ita kuwa kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa, ta ce :

 “Saboda mummunan kisan kiyashin da ‘yan sahyoniyawan sukayi da maraicen nan a kan matsugunnan ‘yan gudun hijirar, muna kira ga al’ummar mu da ke gabar yamma da kogin Jordan da Kudus da yankunan da aka mamaye da kuma kasashen waje da su tashi tsaye domin nuna fishi.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce motocin daukar marasa lafiya sun yi jigilar “yawan mutanen da suka mutu ko kuma suka jikkata a harin.

Kungiyar likitoci marar iyaka ta Doctors Without Borders ta sanar a shafinta na ”X” cewa “bayan harin da Isra’ila ta kai motocinsu na daukar marasa lafiya sun kwashi mutane da suka jikkata da kuma wasu sama da 15 da suka mutu.

A nata bangaren, Isra’ila ta tabbatar da cewa daya daga cikin jiragen sojinta ya “kai hari a wani sansanin Hamas da ke Rafah inda wasu jiga kwamandojin Hamas ke gudanar da ayyukansu”, ciki har da shugabanni biyu na kungiyar a gabar yammacin kogin Jordan, Yacine Rabia da Khaled Nagar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “An gudanar da aikin ne a kan halaltattun manufofi a karkashin dokokin kasa da kasa, ta hanyar amfani da bayanan sirri da ke nuna yadda kungiyar Hamas ke amfani da yankin.”

Game da abinda ya faru, ta nuna “ta na sane da bayanan samun fararen hula da suka jikkata”. 

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke kara kaimi wajen kai farmaki a Rafah, Duk da hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke ranar Juma’a inda ta umarci Isra’ila da ta dakatar da ayyukanta a wannan fanni, wanda ke da muhimmanci wajen shigar da kayan agaji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments