Hare-haren Hizbullah Sun Jazawa HKI A Fagen Gona Asarar Dala Miliyan 108

Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai

Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023.

Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon.

Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman manoma yin hijira.

Bugu da kari, binciken ya ce, barnar da yakin ya haddasa akan gonaki, ya haddasa koma baya a fagen samar da abinci, da kuma kawar da daidaito a kasuwanni.

Shugabar zartarwa ta kungiyar “ReGrow Isra’el” Danil Abraham,  ta sanar da cewa; Barnar da aka samu a kan iyaka da Lebanon tana da girman gaske, da kuma rikiritarwa, ta kuma shafi yanki mai girma fiye da fagen dagar Gaza.

Abraham ta kuma ce; Sai 9000 aka kai wa arewacin “HKI” hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki, da hakan ya sa gonaki masu yawa su ka kone. Haka nan kuma kaso 60% na manoman a Arewacin HKI, sun dakatar da ayyukansu baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments