Search
Close this search box.

Haniyah ya tattauna da masu shiga tsakani a kokarin kawo karshen kisan kiyashi a Gaza

Shugaban ofishin siyasa na Hamas ya tuntubi masu shiga tsakani na Qatar da Masar game da kokarin da ake yi na cimma yarjejeniyar sulhu da

Shugaban ofishin siyasa na Hamas ya tuntubi masu shiga tsakani na Qatar da Masar game da kokarin da ake yi na cimma yarjejeniyar sulhu da za ta iya kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau  Alhamis.

Sanarwar ta ce “A cikin ‘yan sa’o’i na baya-bayan nan, Ismail Haniyeh ya tatatuna ta waya da ‘yan uwan ​​masu shiga tsakani na  Qatar da Masar,” in ji sanarwar.

Tattaunawar ta yi tsokaci ne kan batutuwa da kuma mahangar kan tattaunawar da ake yi, da nufin cimma yarjejeniyar da za ta kawo karshen mummunan zaluncin da ake yi wa mutanen Gaza marasa kariya, wanda yahudawan Isra’ila tare da taimakon manyan kasashe masu girman kai suke aiwatarwa.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata ne gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar da yaki bayan farmakin guguwar Al-Aqsa, wani harin ramuwar gayya da kungiyoyin gwagwarmaya na Gaza suka yi, inda aka kama daruruwan yahudawa.

Ya zuwa yanzu dai Isra’ila ta kashe Palasdinawa kusan 38,000, yawancinsu mata ne da kananan yara da kuma tsoffi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments