Haniya : Raisi ya jaddada cewa tsayin daka wani muhimmin zabi ne na aikin kwatar ‘yanci

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya gabatar da jawabi a wajen jana’izar shugaban kasar Iran marigayi Ibrahim Raisi da abokan tafiyarsa a

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya gabatar da jawabi a wajen jana’izar shugaban kasar Iran marigayi Ibrahim Raisi da abokan tafiyarsa a jami’ar Tehran.

Haniyeh ya ce: “Mun zo ne a yau da sunan al’ummar Palastinu, da sunan kungiyoyin fafutuka a kasar Palastinu, da sunan Gaza domin mu yi ta’aziyya.”

Ya yi nuni da cewa, “Marigayi shugaban kasa ya tabbatar mana da cewa, batun Palastinu shi ne jigon al’amuran al’ummar musulmi, tsayin daka wani muhimmin zabi ne na aikin ‘yantar da kasar, sannan kuma Iran na ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar Palastinawa, har sai burin al’ummar Falastinu da al’ummar musulmi ya cika”.

Ya kuma jaddada cewa guguwar Aqsa girgiza ce ga yahudawa  Sahayoniya tare da kawo sauyi mai tarihi a matakin duniya.

Haniyeh ya jaddada cewa Gaza za ta ci gaba da tsayin daka har sai an ‘yantar da dukkan kasar, tare da Kudus mai albarka, yana mai cewa “a gaban shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya , muna da tabbacin cewa Jamhuriyar musulunci za ta ci gaba da bin manufofinta da ka’idojinta karkashin inuwar shugabanta , kan goyon bayan Falasdinu da gwagwarmaya”.

A yau Laraba, babban birnin kasar Iran, Tehran, ke yin bankwana da gawawwakin marigayi  Ibrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amir Abdollahian, da abokan tafiyarsu, a daidai lokacin da jama’a da dama suka isa kasar daga kasashen ketare domin halartar wannan janaza a birnin Tehran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments