Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6.
Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa.
Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a hannunta tun cikin yakin tufanul Aksa.
A Zagaye na farko na musayar fursinonin tsakanin Hamas da HKI dai, Hamas ta sake yahudawa 33, a yayinda yahudawan suka saki fursinoni falasdinawa kimani 2000.
Marhala ta karshe bayan musayar fursinoni da gawawwaki shi ne, janyewar sojojin HKI daga zirin gaza, ko yankin philidelpia da kuma maganar sake gina gaza. Bayan da HKI ta rusa gine-gine har 170,000 a cikin shekara guda da watanni 3.