Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa a shirye take da saki fursinonin HKI da Amurka, har ma da gawakin wasu 4, idan HKI ta dawo kan ci gaba da aiwatar da abubuwan da yarjeniyar tsagaita wuta a tsakaninta da HKI.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani Jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin wadanda suke tsakanin kungiyar da HKI ne ya bata wannan shawarar, sannan ya kara da cewa, sai dai wannan matakin yana da sharudda, kuma sune HKI ta amince ta dawo kan tattaunawa marhala ta biyu don aiwatar da yarjeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.
Taher al-Nounou ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa kan cewa Hamas zata salami Edan Alexander wanda yake dauke da passport na Amurka da kuma wasu 4 wadanda suke dauke da Passport na kasashen biyu wato HKI da kuma Amurka. Amma tare da wannan sharadin.
Sanarwan ta kammala da cewa kungiyar ta fara sabuwar tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Talatan da ta gabata sannan tawagar HKI ma tana halattar tattaunawan wand aba kai tsaye ba.