Hamas Ta Zargi Blinkin Da Boye Matsayin HKI Kan Takardun Sulhun Shugaba Biden Na Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar Hamas wacce take gwagwramaya da HKI a Gaza, ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken yana yada labarin cewa HKI ta

Kungiyar Hamas wacce take gwagwramaya da HKI a Gaza, ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken yana yada labarin cewa HKI ta amince da shirin shugaba Biden na Sulhu a Gaza, amma kuma ba wanda ya ji jami’in gwamnatin Natanyahu ko guda yana maganar amincewa da shirin ba.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa rashin fitowar wani jami’i ko guda a gwamnatin HKI wanda zai tabbatar da maganar Blinken ya nuna cewa HKI bata amince da shirin sulhun ba.

Kungiyar ta bayyana cewa ta amince da wannan shirin sulhun tare da gabatar da wasu gyare gyare a cikinta. Kungiyar tace ta amince da tsagaita budewa juna wuta na din din din da janyewar sojojin HKI gaba daya daga yankin gaza, da shirin sake gina gaza da kuma shigo da kayakin agaji gaggawa zuwa dukkan yankunan gaza, harila yau da komawar dukkan mutanen da aka kora daga gidajensu a gaza, su koma gidajensu.

Ta kammala da cewa ba abinda take ganin a yanzun a Gaza in banda kara yawan budewa juna wuta tsakanin bangarorin biyu.  Don haka akwai shakku kan yiyuwar tabbatar wannan shirin.

Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar data gabata ce HKI ta fara kaiwa Falasdinawa a Gaza hare hare, wanda ya zuwa yanzu sun kashe mutane fiye da 37,000 a gaza kadai sannan wasu daruriwa a yankin yamma da kogin Jordan . Har’ial yau  wasu akalla 85 000 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments