Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi watsi da zargin da Amurka ta yi mata a baya bayan nan na cewa mayakanta sun

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi watsi da zargin da Amurka ta yi mata a baya bayan nan na cewa mayakanta sun wawushe kayayyakin agaji da wata mota take dauke da shi a yankin Gaza, ta bayyana zargin a matsayin karyace kawai mara tushe balle madafa, tace Amurka na wannan zargin ne domin fakewa da shi wajen takaita shigar da kayyakin agaji a yankin gaza,

Wannan yana nuna karuwar takaddama tsakanin Amurka da sauran bangarorin falasdinawa kan batun samar da kayayyakin agaji da kuma daukar nauyin da ya rataya a wuyansu, gannin yadda tallafi yayi karance kuma kayayyakin more rayuwa sun tabarbare don haka irin wadannan zarge-zarge na iya kara tsananin rashin yarda da kuma kawo cikas a kokarin da ake yi na kai kayayyakin agaji zuwa yankin.

Mashahanta suna kallon labarin Amurka a matsayin wani bangare na parfagandar na canza sunan Hamas da kuma share fagen kwance dammararta, suna ganin cewa wannan ikirarin yana zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin diplomasiya don canza yanayin tsarin gwamnati bayan yakin Gaza, da kuma raunana kungiyoyin gwagwarmaya karkashin kula da aikewa da kayayyakin agaji da aka bujiro da shi

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments