Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mayar da martani ga suka daga Amurka dangane da jan kafa wajen amincewa da kudurin tsagaita bude wuta.
Hamas dai na mayar da martini ne kankalamman sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na cewa it ace ke jan kafa wajen amincewa da kudirin da MDD, ta amince da shi.
Kungiyar ta Hamas na mai cewa ‘’ta yi abin da ya kamata game da tattaunawar zaman lafiya’’.
Hamas ta bayyana cewa ta yi abin da ya kamata dangane da sabuwar shawarar tsagaita bude wuta da kuma duk shawarwarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” inda ta banbanta matsayinta da Isra’ila, wanda ta ce ba ta fito fili ta bayyana amincewa da shirin tsagaita bude wutar ba.
Ko a gefen taron G7 a Italiya, Shugaban Amurka Joe Biden ya zargi Hamas da kawo cikas ga duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta.
“Na gabatar da shawarar da kwamitin sulhu, da G7, da kuma Isra’ila suka amince da ita, amma babban abin da ke kawo cikas a wannan mataki shi ne Hamas da ta ki sanya hannu, duk da cewa sun gabatar da wani abu makamancin haka,” in ji Biden.
Mista Biden dai ya gabatar da wannan shiri ne da sunan Isra’ila, Sai dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ga ganin akwai gibi a yarjejeniyar inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na rusa Hamas tare da kubutar da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.
A nata bangaren, Hamas ta aikewa kasashen da ke shiga tsakani martanin farko wanda ba a bayyana ba.
A cewar wata majiya da ke kusa da tattaunawar, tana kunshe da “gyare-gyare” kan shirin, ciki har da “jaddawalin tsagaita bude wuta na dindindin da kuma janyewar sojojin Isra’ila baki daya daga Gaza.” Bukatun da Isra’ila ke kin amincewa dasu a ko yaushe.