Hamas: Isra’ila Tana Shirin Kashe Falasdinawa A Gaza Da Yunwa

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta yi gargadin cewa HKI tana shirin samar da yunwa mafi tsanani a cikin falasdinawa a Gaza,

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta yi gargadin cewa HKI tana shirin samar da yunwa mafi tsanani a cikin falasdinawa a Gaza, bayan da ta rage yawan abincin tallafin da ke shigowa yankin da rabi ko fiye da haka.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto mai magana da yawun kungiyar Hazim Qasim yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, HKI tana kara tsuke yawan abinda da ke shigowa zirin Gaza, wanda dama don rike Falasdinawa a raye ne kawai, ta kara rage shi zuwa kasa da rabin abincin da suke bukata don rayuwa. Kuma kasa da abinda aka cimma da ita a yarjeniyar tsagaita wuta na shekara ta 2024.

Qasem ya kara da cewa, a labaran da suke isowa daga abinda suka kira cibiyar kula da abinci da taimakon da suke shiga gaza, sun tsaida shawarar kara tsuge yawan abinda da tallafin da ke shigowa gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted