Hamas Ta Yabawa Tarayyar Afirka Kan Yin Tir Da Kisan Kare Dangin Isra’ila A Gaza

Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar

Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa.

Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza.

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”.

Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu

Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha.

A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar shirun da kasashen duniya suka yi dangane da halin da ake ciki a Gaza.

Shugaban Hukumar ya ce: Sun ga yadda duniya ta yi shiru duk da wannan mummunan yanayi da al’ummar Gaza ke ciki, har ma wasu daga cikinsu na yin kira da a kori Falasdinawa daga muhallinsu, lamarin zai kara ta’azzara mummunan kangin da Falasdinawa suka shiga.    

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments