Kungiyar Hamas wacce take fafatawa da sojojin HKI a Gaza ta yi kira ga Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma yankin da aka mamaye a shekara 1948 da su fito don halattar sallar jumma’a da kuma kare farfajiyar masallacin al-aksa a ranar Lahadi da litinin daga keta al-farman masallacin.
Kamfanin dillancin labaran ‘Falasdin Shihab’ ya nakalto majiyar kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa fitowa zuwa masallacin, wanda shi ne masallaci mafi alfarma a addinin musulunci batan Makka da madina, yana daga cikin ayyukan jihadi a kan tafarkin All..
A ranakun Lahadi da Litinin masu zuwa ne, yayan wata kungiyar yahudawan Sahyoniy, wacce ake kira ‘Jama’ar Haikal’ suke shirin gudanar da bukukuwan da suke kira ‘Layya’ a cikin farfajiyar masallacin.
Kungiyar ta yi kira ga matasa da duk wanda zai iya su fara itikafi a cikin masallacin don hana yahudawan keta al-farmansa a cikin yan kwanaki masu zuwa.
Daga karshe kungiyar ta bukaci dukkan musulmi a ko ina suke a duniya, da kuma masu rajin kare hakkin bil’adama da kasashe masu yenci su yi duk abinda zasu yi don maidawa Falasdinawa hakkinsu da aka kwace da kuma kawo karshen mamayar da yahudawan sahyoniyya sukewa kasarsu tun ffiye da shekaru 75 da suka gabata.