Hamas Ta Amince Da Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar Hamas wacce take Jagorantar sauran kungiyoyin falasdinawa a yakin da suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza, ta amince da kudurin kwamitin tsaro na

Kungiyar Hamas wacce take Jagorantar sauran kungiyoyin falasdinawa a yakin da suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza, ta amince da kudurin kwamitin tsaro na MDD na tsagaita budewa juna wuta a gaza da kuma shirin zaman lafiya wanda gwamnatin kasar Amurka ta gabatar.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan jim kadan bayan da mambobin kwamitin tsaro na MDD 15 suka  amince da kudurin da gwamnatin Amurka ta gabatar a jiya litinin dangane da hakan.

Kungiyar ta kara da cewa ta amince da abinda ya zo cikin kudurin na tsagaita budewa juna wuta na din din din a Gaza wanda ya zo cikin kudurin, hakama ta amince da jinyewar sojojin HKI gaba daya daga Gaza, da kuma musayar fursinonin a tsakanin bangarorin biyu.

Banda haka kungiyar ta ce ya amince da shirin sake gida zirin gaza da kuma komawar dukkan Falasdinawa zuwa yankunan a Gaza daga inda aka koresu bayan fara yakin a cikin watan octoban da ya gabata. Hamas ta ce bata yarda da duk wani sauyi a tsarin da yankin gaza yake. Ko kuma rage fadi ko fitar da wani bangare na gaza daga hannun Falasdinawa. Sannan daga karshe ta amince da shigarda kayakin agajin gaggawa zuwa Gaza.

Hamas ta bayyana cewa a shirye take ta bada hadin kai ga masu shiga tsakanin don ganin an aiwatar da dukkan wadannann al-amura wadanda suka zo cikin wannan kudurin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments