Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji.
Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin da Netanyahu ya dauka na dakatar shigar da kayan agaji cikin Gaza, wata tsokana ce, kuma laifin yaki ne sannan uwa uba keta yarjejeniyar datakar da wuta da musayar fursunoni ce.
Bugu da kari, kungiyar ta Hamas ta ce bukatar da Netanyahu ya gabatar na tsawaita zango na farko na yarjejeniyar, wani yunkuri ne na gujewa aiwatar da ita kanta yarjejeniyar.
Haka nan kuma Hamas ta bukaci Amurka da ta daina zama mai goyon bayan manufofin Netanyahu, tana mai jaddada cewa duk wani kokari na take hakkokin Falasdinawa ba zai haifar da da, mai ido ba.