Hamas da Islamic Jihad Sun Taya Sheikh Naim Qassem Murna Zama Sabon Shugaban Hizbullah

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu, Hamas da Islamic Jihad sun taya Sheikh Naim Qassem murna a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon. A cikin wata

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu, Hamas da Islamic Jihad sun taya Sheikh Naim Qassem murna a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar Hamas ta taya Sheikh Naim Qasem murna kan mukamin na babban sakataren kungiyar Hizbullah.

An bayyana cewa, nada Sheikh Naim Qassem a matsayin babban sakataren Hizbullah, zai farfado da kungiyar bayan shahadar Sayyid Hasan Nasrallah.

Hamas ta kara da cewa: Muna kara jaddada matsayinmu ga sabon shugaban kungiyar Hizbullah, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimake shi ya ci gaba da tafarkin jihadi da tsayin daka.

A nata bangaren kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinawa ta taya Sheikh Naim murna inda ta ce nadin lamari ne da ke nuni da irin karfin gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon. »

A jiya Talata ne aka zabi mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qassem a matsayin sabon shugaban kungiyar inda zai gaji Sayyed Hassan Nasrallah wanda ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut a watan jiya.

Sheikh Qassem wani jigo ne a kungiyar Hizbullah, wanda ke rike mukamin mataimakin sakatare janar na kungiyar tun shekara ta 1991.

Ya halarci tarukan da suka kai ga kafa kungiyar Hizbullah a shekarar 1982.

Sheikh Qassem ya dade yana daya daga cikin manyan masu magana da yawun kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments