Habasha da Dangote sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun  takin zamani a duniya a garin Gode.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari.

Ana has ashen cewa idan an kammala aikin,  zai kasance cikin  manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara.

A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin watanni 40 kuma zai hada da bututun jigilar iskar gas daga filayen gas na Calub da Hilala na Habasha.

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed wanda ya halarci rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na samun ‘yancin cin abinci daga kokari da gumin ‘yan Afirka.

A nasa bangaren, Aliko Dangote ya ce hadin gwiwar ya nuna hangen nesa domin kara habaka masana’antu a Afirka da kuma inganta samar da abinci a fadin nahiyar.

“Mun kuduri aniyar kawo kwarewarmu na shekaru da dama a manyan ayyukan masana’antu don tabbatar da cewa wannan kamfani ya zama ginshikin sauye-sauyen masana’antu na Habasha da kuma hanyar samar da amfanin gona a duk fadin yankin,” in ji Dangote.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted