Gwamnatin Najeriya Zata Samar Da Kananan Cibiyoyin Kiwon Lafiya 8,880 A Duka Fadin Kasar

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa ta ware kudade don gina kananan cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin kasar. Jaridar daily Trust ta Najeriya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa ta ware kudade don gina kananan cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin kasar.

Jaridar daily Trust ta Najeriya ta nakalto mataimakin shugaban kasa Alhaji Shetima yana fadar haka a ranar Asabar a lokacinda yake kaddamar da cibiyar yaki da cutar daga a cikin asbitin koyon aikin likitanci ta OOUTH dage birnin shagamu na jihar Oyo.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa shirin gina wadannan kananan cibiyoyin kiwon lafiya dai yana daga cikin babban shirin gwamnatin mai ci na kyautata cibiyoyin kiwon lafiya a kasar gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments