Search
Close this search box.

Gwamnatin Najeriya Ta Sha Alwashin Kubutar Da Mutanen Da Aka Sace

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanar da cewa zatayi iya kokarinta don ganin ta kwato dukkan mutanen da akayi garkuwa dasu a baya baya nan. Wata

Gwamnatin Tarayyar Najeriya, ta sanar da cewa zatayi iya kokarinta don ganin ta kwato dukkan mutanen da akayi garkuwa dasu a baya baya nan.

Wata sanarwa da ministan yada labarai na kasar ya fitar ta ce gwamnatin tarayya ta sha alwashin hada karfi da karfe don ganin an kubutar da daliban makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kuriga dake jihar Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira na karamar hukumar Ngala ta jihar Borno da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.

Mohammed Idris, Ya ce gwamnati tana Alla-wadai da duk wani nau’i na tashin hankali ko afka wa jama’a da ba su ji ba ba su gani ba, musamman marasa galihu.

Yayin da yake jajantawa iyalai da kuma al’ummar da abin ya shafa, Idris ya ce shugaban Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta ganin an ceto dukkan wadanda aka sace, tare da kamo wadanda ke da hannu a wannan danyen aiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments