Gwamnatin Masar Ta Gargadi ‘Yan Kasarta Da Suke Somaliland Saboda Rikicin Yankin

Gwamnatin Masar ta bukaci ‘yan kasarta da su fice daga Somaliland cikin gaggawa Ofishin jakadancin Masar da ke Mogadishu ya gargadi dukkan ‘yan kasar Masar

Gwamnatin Masar ta bukaci ‘yan kasarta da su fice daga Somaliland cikin gaggawa

Ofishin jakadancin Masar da ke Mogadishu ya gargadi dukkan ‘yan kasar Masar kan nisantar yin balaguro zuwa yankin Somaliland a Jamhuriyar Somaliya, tare da lura da cewa gargadin ya zo sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a yankin da kuma tasirinsa ga tsaron lafiyarsu.

Ofishin jakadancin ya yi kira ga ‘yan kasar ta Masar da ke yankin da su hanzarta barin yankin cikin gaggawa ta hanyar filin jirgin saman Hargeysa, yana mai jaddada cewa: Halin da ake ciki na tsaro yana hana ba da duk wani taimako daga ofishin jakadancin Masar ga ‘yan kasar ta Masar a can.

Ofishin jakadancin Masar ya kuma jaddada yin kira ga ‘yan kasar Masar da ke son ziyartar kowane yanki na Jamhuriyar Tarayyar Somaliya da su bi ka’idoji da tsare-tsare da hukumomin da suka dace a Tarayyar Somaliya suka tsara.

Wannan gargadi dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin kahon Afirka, musamman a kasar Somaliya, wadda ta zama fagen gasar kasashen Masar da Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments