Ministan harkokin wajen kasar Labanon ya gargadi kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan illar da ke tattare da rashin hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila a gaban kuliya
Ministan harkokin wajen kasar Lebanon Abdallah Bouhabib ya yi gargadi a gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa: Babu wanda ke cikin aminci a wannan duniya bayan hare-haren baya-bayan nan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Lebanon ta hanyar na’urorin sadarwa na ICOM kirar kasar Japan.
Abdullah Bouhabib ya tabbatar da hakan a jawabin da ya gabatar yayin zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa: Idan wannan ta’addancin ya wuce ba tare da la’akari da shi ba a majalisar ta Dinkin Duniya, kuma ba tare da an hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila ba, kuma ba a binciko wadanda suka shirya makircin aikata hakan ba, kuma ba a yanke musu hukunci a matsayin hukunta su ba domin tilasta dakatar da ire-iren wadannan hare-haren wuce gona da iri ba, to, lallai al’ummun duniya zasu yi watsi da amincin wannan Majalisar ta kasa da kasa, da kuma nuna ko-o-ho kan batun kare hakki da ‘yancin ɗan adam.
Bou Habib ya ce: Shin wannan ba hakikanin ta’addanci ba ne, yayin da aka kai hari ga duk jama’ar kasa gaba daya, Shin abin da ake bukata ke nan a yau kawar da al’ummar Lebanon baki daya tare da hukunta gaba daya al’ummarta a matsayin hukunci na gama-gari?