Gwamnatin Iran Ta Kira Yi Al’ummar Kasar Da Su Fito Domin Halartar Jerin Gwanon Ranar Kudus

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malama Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malama Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar Kudus ta duniya, wacce take fatan ganin ta taka rawa wajen taimakawa al’ummar Falasdinu.

Muhajirani wacce ta yi bayanin haka a wata hira ta tashar talbijin ta kuma kara da cewa; Gwargwadon yadda al’umma za su fito wajen yin jerin gwanon saboda hadakar da ake da ita a tsakanin al’ummar Iran da Falasdinawa ta fuskokin addini da al’adu, da kuma tarayya akan manufofin juyi, tasirin haka zai fi fitowa.

Malama Fatima Muhajirani ta kuma ambato maganar Imam Khumaini     ( r.a) akan fatansa na ganin an sami fitowa mai yawa domin karfafa al’ummar Falasdinu.

A na gudanar da jerin gwanon ranar Kudus ta kasa da kasa ne a kowace ranar juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments