Gwamnatin Iraki Ta Sanar Da Makoki Na Kwanaki 3 Kan Shahadar Sayyid Nasrallah

Firaministan kasar Iraki Muhammad Shi’a Al-Sudani ya ayyana zaman makoki na gama-gari a fadin kasar ta Iraki na tsawon kwanaki uku domin tunawa da shahadar

Firaministan kasar Iraki Muhammad Shi’a Al-Sudani ya ayyana zaman makoki na gama-gari a fadin kasar ta Iraki na tsawon kwanaki uku domin tunawa da shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah.

Firaministan kasar Iraki Muhammad Shi’a Al-Sudani ya yi alhinin shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Hassan Nasrallah tare da tabbatar da matsayin kasar Iraki na tsayawa tsayin daka da al’ummar Palastinu da na Lebanon.

Ya ce: “A wani sabon hari na laifin yaki, da kuma laifin da ke tabbatar da wuce gona da iri na sahyoniyawa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon,  Sayyed Hassan Nasrallah, ya kai ga matsayin shahidi a kan tafarkin gaskiya, ya samu mafi alheri a duniya da lahira, kuma ya bi tafarkin jaruman shahidai wadanda suka sadaukar da kansu wajen tunkarar mamaya da zaluncin Isra’ila”.

Ya kara da cewa, “Muna jaddada gargadin mu da kuma mai da hankali kan alhakin da ya rataya a wuyan kungiyoyin kasa da kasa , da manyan kasashen da ke zama mambobi na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma dukkan kasashen da ke da tasiri a yankin, na dakile wuce gona da iri da kuma dakile kisan kare dangi a kan Falasdinawa, wanda Haramtacciyar kasar Issra’ila ke yi.

Ya ce;  abin da ya faru shi ne dama yake faruwa a kan ‘yan uwanmu a Gaza, kuma yake ci gaba da kasancewa a yanzu  akan ‘yan uwanmu na Labanon, don haka ci gaba da kashe-kashe ba tare da nuna bambanci da nufin kashe adadi mai yawa na al’ummar kasar Lebanon ita ce bababr manufar Haramtaccyar kasar Isra’ila, domin ya zuwa daruruwan ‘yan kasar Labanon wadanda ba su ji ba ba su gani ba sun yi shahada a cikin ‘yan kwanaki, don haka ta’addancin a kan fararen hula yake karewa.

Firaministan ya tabbatar da cewa: A wannan rana, matsayin kasar Iraki na tsayawa tsayin daka tare da al’ummar Palastinu da na Lebanon ne, kuma wannan matsaya ta ginu ne a kan halaccin kasa da kasa da ka’idojin jin kai da kyawawan dabi’u da ke bukatar goyon bayan al’ummomin duniya.

A daya bangaren  yau Asabar, ofishin babban malamin Iraki  Sayyid Ali al-Sistani ya gabatar da ta’aziyya ga shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah, ya kuma jaddada cewa babban shahidin ya kasance abin koyi na jagoranci wanda ba a cika samun irinsa ba, kuma an ga hakan a cikin ‘yan shekarun nan.

Ofishin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Mun yi matukar bakin ciki da jin  labarin shahadar malami Hujjat al-Islam wal-Muslimeen, Sayyed Hassan Nasrallah, da wani gungun ‘yan’uwansa da ke gwagwarmayar a Lebanon, da dimbin wadanda ba su ji ba ba su gani ba fararen hula a cikin mummunan kisan kiyashin da sojojin makiya yahudawan sahyoniya suka yi a kudancin birnin Beirut.”

Bayanin Ya kara da cewa: Babban shahidi ya kasance abin koyi ya taka rawar gani wajen samun nasarar ‘yantar da kasar Labanon da hanyar ‘yantar da kasar Iraki tare da tallafa wa Iraki da duk abin da ya dace wajen ‘yantar da kasarsu. A kan ‘Yan ta’addan ISIS kuma ya dauki matsayi mai girma. Wajen  tallafawa al’ummar Palastinu da ake zalunta kuma ya gabatar da rayuwarsa domin ‘yanci Falastinu da al’ummarta da wuraren musulmi masu tsarki da suke ciki wannan kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments