Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila.
Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza.
Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda ake tsare da su da hakan ke kara masifar azabtarwar da ake gana musu. Haka kuma wanda ake tsare ana yi masa fyade a gaban ’yan uwansa da ake tsare da su, da nufin wulakanta shi da kuma rusa tunaninsa, da hakan ke kara tsoro da firgici a tsakanin sauran wadanda ake tsare da su.