Guterres: Dole Ne Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Gaggauta Janye Shirinta Kan Gaza

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari.

A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin neman shinfida cikakken ikon mallakar garin Gaza daga arewacin yankin, Turk ya ce hakan ya saba wa hukuncin da kotun duniya ta yanke na cewa dole ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta kawo karshen mamayar da take yi cikin gaggawa tare da cimma matsaya guda biyu da aka amince da ita da kuma ‘yancin cin gashin kai da Falasdinawan suke da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted