Guteress : Hari Kan Dakarun MDD, Zai Iya Zama Laifin Yaki

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, hare-haren kan dakarun wanzar da zaman lafiya na iya zama ‘laifi na yaki’. “Hare-hare” kan dakarun wanzar da

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, hare-haren kan dakarun wanzar da zaman lafiya na iya zama ‘laifi na yaki’.

“Hare-hare” kan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kan iya zama “laifukan yaki”, kamar yadda kakakin babban sakataren MDD ya yi gargadi, bayan wani sabon taho mu gama da akayi tsakanin sojojin Isra’ila da na MDD a kudancin Lebanon.

“Sakataren Janar na MDD, Antonio Guterres, ya sake maimaita cewa ma’aikata da wuraren dakarun UNIFIL (Rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon) ba zai yi wu ana kai musu hari ba.

Hare-haren da ake kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya keta dokokin kasa da kasa ne, da na jin ne, wandada za su iya zama laifin yaki, ”in ji, Stéphane Dujarric.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa-rana tsakanin MDD da Isra’ila wacce hare-harenta suka jikkata dakarun wanzar da zaman lafiya a wani bude wuta kan hedikwarsu dake kudancin Lebabon har sau biyu a jere a makon da ya shude.

Bayan hakan kuma tankokin yakin Isra’ila sun yi amfani da karfi wajen kutsawa a wurin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD, tare da jefa musu hayaki mai sa hawaye.

Majalisr Dinkin Duniya dai ta yi allawadai da harin da aka kai wa jami’an nata, kuma ta je dakarun Isra’ilan sun kutsa kai da karfi ne a cikin ofishin jami’an nata a ranar Lahadi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments