Gungun Kasashen 18 A MDD, Sun Ce Harin Isra’ila Kan Iran Ya Keta Dokokin Kasa da Kasa

Gungun kawayen da ke kare kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai a baya-bayan nan a kan Iran, cin

Gungun kawayen da ke kare kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai a baya-bayan nan a kan Iran, cin zarafi ne ga kundin tsarin mulkin MDD, da muhimman ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma ‘yancin kan kasa da kuma ‘yancin kai na kasar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, gungun mai mambobi 18 a Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka kan Iran a ranar 26 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin shahadar wasu jami’an soji hudu da kuma farar hula guda.

gungun yace harin ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta yin barazana ko amfani da karfi a kan iyakokin kasashen.

Haka kuma ya bayyana matukar damuwarsa game da ci gaba da kokarin da gwamnatin Isra’ila ke yi na ruruta wutar yaki a yammacin Asiya da kuma kunna wuta a yankin.

Sanarwar ta ce “Kamar yadda ake ci gaba da keta dokokin kasa da kasa akai-akai, tsokana da cin zarafi da gwamnatin Isra’ila ke yi kan kasashen yankin na nuna aniyar ta na tada zaune tsaye.”

Ta kuma jaddada wajabcin gaggauta dorawa gwamnatin Isra’ila alhakin dukkan laifukan da take aikatawa kan al’ummar falastinu da sauran kasashen larabawa a yankunan da ta mamaye da ma yankin baki daya.

Babban makasudin hada wannan kungiya shi ne tallafawa Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma zama wani dandali, a tsakanin sauran abubuwa, don inganta yaduwar doka fiye da karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments