Ghana Ta sanar Da Sabon Shirin Inganta Rayuwar ‘Yan Kasarta

Ministan Kudi na Ghana, Casil Ato Furson, ya sanar da cewa kasar za ta zuba jarin dala biliyan 10 a cikin shekaru hudu, tun daga

sabon shirin Ghana

Ministan Kudi na Ghana, Casil Ato Furson, ya sanar da cewa kasar za ta zuba jarin dala biliyan 10 a cikin shekaru hudu, tun daga shekarar 2027.

A cikin sabon shirin  Tattalin Arziki, wanda za a aiwatar ta hanyar kuɗaɗen shiga na cikin gida don haɓaka samarwa kayayyaki da kuma fitar da su, gami da samar da ayyukan yi.

Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin 2027 ga majalisar dokoki, Furson ya ce shirin zai mayar da hankali kan noma na kasuwanci, kayayyakin more rayuwa na makamashi, fasaha, masaku, da kuma sarrafa ma’adanai masu mahimmanci, da sauran fannoni.

Ya yi alƙawarin cewa, “Gwamnati za ta kiyaye kwanciyar hankali, samar da ababen more rayuwa, shirya ayyukan da za a iya amfana da su a bankuna, da kuma ƙirƙirar yanayi don samun ayyuka.”

A cewar Reuters, kasafin kuɗi ya nuna ci gaban GDP da kashi 5.2% a shekara mai zuwa, daga kashi 4.8% a shekarar 2026, da kuma gibin kasafin kuɗi na kashi 3.6% na GDP, wato ƙasa da kashi 4% a wannan shekarar.

Gwamnati kuma tana shirin ci gaba da rage hauhawar farashin kayayyaki da kashi 8%.

Wannan kasafin kuɗi shi ne na farko tun bayan da Ghana ta kammala shirin tallafawa na dala biliyan 3 daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), wanda ya haifar da gagarumin ci gaba a tattalin arziki a cewar mahukuntan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted