Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu

Ministocin tsaro da muhalli na Ghana na daga cikin mutane takwas da suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar

Ministocin tsaro da muhalli na Ghana na daga cikin mutane takwas da suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar wannan Laraba, kamar yadda fadar shugaban kasar ta tabbatar, bayan da rundunar sojin kasar ta bayar da rahoton cewa jirgin ya fita daga tsarin tantacewa na na na’urar radar.

Lamarin dai ya jefa al’ummar kasar cikin firgici tare da sanar da makoki a dukkanin fadin kasar a hukumance.

Ministan tsaro Edward Omane Boamah ya hau kan mukaminsa ne bayan rantsar da Shugaba John Mahama a watan Janairu. Sai kuma Ministan Muhalli, Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed, wanda  shi ma yana cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin.

Shugaban ma’aikata Mahama Julius Debrah ya ce “Shugaban kasa da gwamnati suna mika ta’aziyyarmu da jajantawa ga iyalan ‘yan uwanmu da ma’aikatan da suka rasa rayukans a hidimar kasa,” in ji Julius Debrah, kamar yadda kuma  hukumomi suka tabbatar da cewa babu wanda ya tsira a hatsarin.

Wannan lamari dai ya auku ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan karuwar  barazanar kungiyoyin ‘yan ta’ada masu ikirarin  jihadi a kan iyakar Ghana da Burkina Faso da ke arewacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments