Jaridar Maariv ta Isra’ila ta yi hasashen cewa, Hizbullah ta yi nisa matuka wajen jurewa fuskantar kowane irin yanayi, kuma ruwan wuta da kisan da take yi wa sojojin Isra’ila ya tabbatar da cewa tana nan da karfinta kuma rusa ta ba a abu ne mai yiwuwaba, sabanin bayanan leken asiri da banagaren Isra’ila ke bayarwa, in ji jaridar Maariv.
Yanayin da Hizbullah take ciki na kara tsananta hare-hare a kan Isra’ila, shi ne ya kara bata karfin gwiwa wajen kin amincewa da bukatun “Isra’ila” na neman a tsagaita bude wuta.
Jaridar ta kara da cewa, “Isra’ila na fafutukar ganin ta sanya sharuddanta a kan kungiyar Huzbullah, tare da nemana dakatar da bude wuta a bisa wadannan sharudda, wanda kuma tuni Hizbullah ta yi watsi da hakan.
Maariv ta ci gaba da cewa, kungiyar Hizbullah ta shirya yaki na lokaci mai tsawo, tana mai ishara da cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, bai nuna sassauci ba wajen batun shawarwarin tsagaita bude wuta.
Jaridar ta yi nuni da kalaman Sheikh Qassem daga jawabinsa na farko a matsayin Sakatare-Janar na Hizbullah, wanda ke tabbatar da karfin kungiyar na ci gaba da yaki na tsawon lokaci ba tare da gajiyawa ko ja da baya ba.
Sannan kuma jaridar ta yi ishara da wasu muhimman abubuwa da ke nuni da cewa Hizbullah tana yi wa Isra’ila barna, inda a halin yanzu ta samu nasarar halaka adadi mai yawa na sojojin kundubala na Isra’ila wato rundunar Golani, kamar yadda kuma koa kwanakin baya kungiyar ta kai hari a kan gidan Netatanyahu wanda ya tsallake rijiya da baya, kamar yadda kuma mayakan kungiyar sun tislasta yahudawan Isra’ila da ke arewa kauracewa garuruwansu tare da mayar da su suna rayuwa a cikin ramuka da aka gina domin tsira da rayukansu, wanda dukkanin wadananna bubuwa na nuni ne da karfin kungiyar ta Hizbullah.