Gaza : Yara 351 Suka Mutu Tun Bayan Tsagaita wuta_Unicef

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa kusan dukkan yara a Gaza suna bukatar tallafi.

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya sanar a cikin wata sanarwa cewa an kashe yara Falasdinawa 351 a yankin Gaza tun bayan da aka sanar da tsagaita wuta a watan Oktoban 2025.

Kamfanin dilancin labaren IRNA, wanda ya ambato kafafen yada labaran Falasdinawa, ya rawaito Edward Beigbeder, Daraktan Yankin UNICEF na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, ya yi kira a cikin sanarwar da hukunta wadanda ke da alhakin mutuwar yara da raunuka da suka haifar da nakasa ta dindindin.

Da yake lura da cewa a cikin kwanaki shida da suka gabata kadai, an kashe yara takwas sannan wasu 20 suka jikkata, ya jaddada cewa dole ne gwamnatin Sahayoniya ta dauki matakai masu inganci don hana ci gaba da tashin hankali, girmama bambance-bambance tsakanin manufofin farar hula da na soja, da kuma tabbatar da kariya ta musamman ga yara, bisa ga dokokin jin kai na kasa da kasa.

M.Beigbeder ya kara da cewa wannan matakin cin zarafin yara ba za a yarda da shi ba kuma yaran da suka tsira daga hare-haren suma sun fuskanci manyan cikas a kan hanyarsu ta samun murmurewa ta jiki da ta hankali saboda rugujewar tsarin kiwon lafiya na Gaza.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa kusan dukkan yara a Gaza suna bukatar tallafi, yayin da ake ci gaba da tilastawa ‘yan gudun hijira barin gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted