Gaza : Spain Ta Soke Cinikin Makamai Da Wani kamfanin Isra’ila

Gwamnatin Spain ta sanar da soke wata kwangilar cinikin makamai da wani kamfanin Isra’ila, saboda yakin da ta ke ci gaba da yi kan al’ummar

Gwamnatin Spain ta sanar da soke wata kwangilar cinikin makamai da wani kamfanin Isra’ila, saboda yakin da ta ke ci gaba da yi kan al’ummar falasdinu a zirin Gaza.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Spain ta sanar a ranar Talata cewa “Gwamnatin kasar tana kan bakarta na cewa  ba za ta sayar da makamai ga Isra’ila ba tun bayan barkewar rikici a yankin Gaza.”

Daruruwan masana da masu fada a ji a Spain ne suka rubuta wasika zuwa ga Firayim Minista Pedro Sanchez, suna kira da a kakabawa Isra’ila takunkumin makamai.

Sun nuna matukar damuwa kan ci gaba da cinikin makamai da kayan soja da kasar Spain ke yi da Isra’ila.

“Sun bukaci gwamnati da ta dakatar da duk wani nau’in cinikin makamai da kayan aikin soji tare da Isra’ila, kuma sun nuna matukar damuwa game da dangantakar soja da Spain da Isra’ila.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments