Gaza : MDD Da Hukumomin Jinkai Na Duniya Sun Yi Gargadi Kan Halin Da Ake Ciki

Shugabanni da hukumomin jinkai na MDD sun fitar da wani gargadi na hadin gwiwa inda suka bayyana halin da ake ciki a arewacin Gaza a

Shugabanni da hukumomin jinkai na MDD sun fitar da wani gargadi na hadin gwiwa inda suka bayyana halin da ake ciki a arewacin Gaza a matsayin marar misali.

Sun ce daukacin al’ummar Falasdinu da ke wurin na fuskantar barazanar mutuwa daga walau dai cututtuka, ko yunwa ko tashin hankali yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari babu kakkautawa.

Rahotanni na cewa ana ganin karin yara da dangi da ke neman taimakon kusan komai ma, kuma ana ci gaba da ganin karuwar wadanda hare-haren ke shafa, ciki har da mata da kananan yara.

Fatan da Amurka ta yi na ganin an tsagaita wuta ta ƴan kwanaki gabanin zaben kasar a mako mai zuwa ya ci tura, hasali ma sai yadda Isra’ila ta zafafa hare-harenta.

Adadin wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a baya-bayan nan tun bayan fara yakin Gaza ya kai 43,314 kuma akasarinsu fararen hula ne, a cewar bayanai daga ma’aikatar lafiya ta gwamnatin Hamas, wadda Majalisar Dinkin Duniya ke ganin abin dogaro ne.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu 102,019 sun jikkata a harin da ake ci gaba da kaiwa.

Ko a baya baya nan sSojojin Isra’ila sun kashe mutum 55 tare da jikkata wasu 192 a kisan kiyashi bakwai da suka yi kan wasu iyalai a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments