Search
Close this search box.

Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 210 A Yau Domin Kwato Yahudawa 4 Da Ake Tsare Da Su

Sojojin Isra’ila sun sake yin wani kisan kiyashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Nusairat  da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla 210

Sojojin Isra’ila sun sake yin wani kisan kiyashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Nusairat  da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla 210 kafin su kwato wasu yahudawa hudu da aka yi garkuwa da su.

Sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a yankin da aka yi wa kawanya a yau Asabar, musamman a ciki da wajen sansanin ‘yan gudun hijira na Deir el-Balah da kuma na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.

Sojojin yahudawan sun kai hari kai tsaye kan fararen hula, ciki har da yara, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin Gaza ya tabbatar.

Ya kara da cewa sun kashe akalla mutane 210 tare da jikkata wasu sama da 400.

An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Al Awda da ke sansanin da kuma Asibitin Shahidan Al Aqsa da ke Deir el-Balah.

Wani mai magana da yawun asibitin Al-Aqsa ya ce adadin wadanda suka jikkata yana da yawa wanda da wuya a iya tabbatar da adadinsu.

Ma’aikatar lafiya ta rubuta a shafin Facebook cewa “da yawan wadanda suka jikkata suna kwance a kasa kuma kungiyoyin likitocin na kokarin ceto su da kayan aiki kalilan da suke da sua  wannan asibiti.”

Ma’aikatar ta fitar da hotuna, da ke nuna majinyata, ciki har da yara, wadanda ke kwance a kasa a asibitin a ciki jini.

Babu wani jami’in Isra’ila da ya ambaci dimbin Falasdinawa da aka yi wa kisan kiyashi a sansanin. Maimakon haka, sojojin yahudawan sun fitar da wata sanarwa, inda suka ce “sun ceto mutane hudu da aka kama kuam ake garkuwa da su a tsakiyar zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments