Gaza : Gwamnatin Nicaragua Ta Yanke Huldar Diflomasiyya Da Isra’ila

Gwamnatin Nicaragua ta sanar da katse huldar diflomasiyya da Isra’ila wacce ta kwashe shekara guda tana yakin kisan kare dangi kan al’ummar Falasdinu a zirin

Gwamnatin Nicaragua ta sanar da katse huldar diflomasiyya da Isra’ila wacce ta kwashe shekara guda tana yakin kisan kare dangi kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.

Mataimakin shugaban kasar Nicaragua Rosario Murillo ne ya sanar da daukar matakin ga kafafen yada labaran kasar a ranar Juma’a.

Rikicin, in ji gwamnatin Nicaragua, yanzu haka kuma “ya kara tsananta kan Lebanon kuma yana matukar barazana ga Syria, Yemen da Iran.”

Isra’ila ta kaddamar da yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta kaddamar da harin ba zata kan ‘yan mamaya a matsayin mayar da martani ga kazamin cin zarafi da Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan.

Hare-haren da gwamnatin kasar ta kai a zirin Gaza ya zuwa yanzu ya kashe akalla Falasdinawa 42,150 tare da jikkata wasu 98,117.

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya yanke huldar diflomasiyya da Isra’ila a watan Mayu, yana mai kiran gwamnatin firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da “kisan kare dangi”.

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva shi ma ya kira jakadan kasar a yankunan da aka mamaye a wannan watan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments