Gaza : Adadin Fararen Hula Da Sukayi Shahada A Hare-haren Isra’ila A Beit Lahia Ya Kai 109

Bayanai daga Falasdinu na cewa adadin falasdinawan da sukayi shahada a harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani gini a yankin Beit Lafia

Bayanai daga Falasdinu na cewa adadin falasdinawan da sukayi shahada a harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani gini a yankin Beit Lafia ranar Talata ya kai akalla 109 da suka hada da mata da kananan yara.

Rahotanni sun ce mutane da dama na ci gaba da kasancewa makale a karkashin baraguzan ginin.

 Daraktan asibitin Kamal Adwan, ya shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa da dama daga cikin wadanda suka jikkata sun isa wurin kuma dayawa daga cikinsu na iya mutuwa saboda karancin kayan aiki.

Ya kara da cewa “Dole ne duniya ta dauki mataki, ba wai kawai kallon kisan kiyashin da ake yi a zirin Gaza ba.”

 “Muna kira ga duniya da ta aiko da tawagogin likitoci na musamman don kula da mutane da dama da suka jikkata a asibiti.”

Kashe-kashen ya zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ta mamaye arewacin Gaza na tsawon makonni, inda ta kashe Falasdinawa sama da 1,000 tare da lalata unguwanni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments