Gaza: Adadin Falastinawa Da Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila Ya Hausa Dubu 40

A cikin wani bayani da ta fitar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce yawan wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren kisan kiyashi na Isra’ila a

A cikin wani bayani da ta fitar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce yawan wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren kisan kiyashi na Isra’ila a yankin yah aura mutane dubu 40.

Bayanin ya ce akalla mutum 40,005 aka kashe a yakin, ciki har da 40 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sannan kuma an jikkata wasu mutane 92,401 a rikicin da ya barke a ranar 7 ga Oktoban shekarar da ta gabata.

Tun daga jiya kasar Qatar  ta karbi bakuncin tattaunawar tsagaita wuta a Zirin Gaza, domin neman cimma yarjejeniyar da ake fatan za ta kai ga dakatar da bude wuta.

Kasashen da ke shiga tsakani na Amurka da Qatar da Masar sun gayyaci Isra’ila da Hamas domin tattaunawa da nufin kawo karshen kisan kare dangi da Isra’ila ke yi kan fararen hula akasarinsu mata da kananan yara a Gaza.

Sai dai tuni Hamas ta sanar da cewa ba za ta halarci taron ba, wanda kuma ta bayyana sakamakonsa da cewa bai yi daidai da abin da aka amince da shi a zaman da ya gabata ba.

Majiyoyi na kusa da masu shiga tsakanin dai sun bayyana cewa, Isra’ila tana ta hankoron ganin ta kawo tarnaki ga wannan tattaunawa, domin samun hujjar ci gaba da kisan gilla take yi a Gaza, ta yadda Benjamin Netanyahu da majalisar ministocin gwamnatin yaki da yake jagoranta, za su ci gaba da kasancewa a kan madafun iko.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments