Fizishkiyan: Ba Za Mu Zauna Kan Teburin Tattaunawa Da Wanda Yake  Yi Mana Barazana Ba

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu.

Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce;  Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta.

Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran  ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da kasashe masu yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments