Search
Close this search box.

Fiye Da Sojojin Isra’ila 7000 Ne Ke Cin Mawuyancin Hali Na Raunin Da Suka ji Sakamakon Haren – haren  Gaza .

Ma’aikatar yaki ta HKI ta fitar da sanarwar cewa  daga ranar 7 ga watan oktoban shekarar da ta gabata zuwa yanzu kimanin sojojin Isra’ila guda

Ma’aikatar yaki ta HKI ta fitar da sanarwar cewa  daga ranar 7 ga watan oktoban shekarar da ta gabata zuwa yanzu kimanin sojojin Isra’ila guda 7000 da 209 ne suke fama da mummunar rauni da suka ji a jiki ko a kwakwalwa dake samun kulawa a Asibitoci sakamakon hare-haren da suka kai a yankin Gaza.  

Haka zalika Ma’aikatar ta kiyasta cewa kashi 30 cikin dari na wannan adadin suna fama da matsalar damuwa da ta kwakwalwa ne, sai dai kafafen watsa labaran gwamnati na rage yawan adadin masu fama da matsalar a cikin sojojin don storon martanin da alummar Isra’ila za su mayar a cikin gida saboda bacin rai.  

Gwamnatin Isra’ila na fuskantar mummunar matsala aciki da waje, domin a tsawon watanni 6 da ta kwashe na kaddamar da yaki a yankin gaza ba ta tsinana komai ba banda kisan kare dangi kan mata da yara kana na da rusa muhimman wurare, da laifukan yaki da suka keta dokokin kasa da kasa da kuma jefa yankin cikin musafar yunwa da fari da karancin ruwa da magani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments