A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 387,sojojin mamayar HKI suna cigaba da tafka laifukan yaki,inda a cikin kwanaki 22 ta kashe Falasdinawa 1000.
Bugu da kari a wannan tsakanin sojojin mamayar HKI sun kashe ‘yan jarida 182,kamar yadda jami’in hukumar agaji a Gaza Muhammad Basal ya bayyana.
A cikin kisan kiyashi na bayan nan da ‘yan sahayoniyar su ka yi sun kai hari a cikin makarantar “Asma” da ‘yan gudun hijira suke ciki a gabar ruwa, inda su ka kashe mutane 10.
A yankunan Jabaloya da Beit Hanun da Beit lahiya adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 100,bayan da ‘yan sahayoniyar su ka rushe gidajen da mutane suke ciki.
Jami’in agaji ya kara da cewa; Sojojin mamayar suna kuma kashe duk wani ma’aikacin agaji wanda yake kokarin kai dauki domin ceto da rayuka.
Har ila yau da akwai wani adadi mai yawa na mutanen Gaza da ba a san makomarsu ba.