Farin Jinin Shugaban Kasar Amurka Yana Raguwa Saboda Nuna Goyon Bayan HKI A Yakin Gaza

Wani sakamakon sauraron ra’ayin jama’a da aka gudanar a cibiyoyi mabanbanta a Amurka yana nuni da yadda karbuwar shugaban kasar Joe Biden ta samu koma

Wani sakamakon sauraron ra’ayin jama’a da aka gudanar a cibiyoyi mabanbanta a Amurka yana nuni da yadda karbuwar shugaban kasar Joe Biden ta samu koma baya matuka saboda yadda gwamnatinsa take nuna goyon baya ga HKI ba tare da wani sharadi ba.

A nata sauraron ra’ayin jama’ar da ta gudanar, mujallar “Newsweek” ta ce; Bayan gushewar watanni shida daga yakin Gaza, ya fito fili cewa al’ummar kasar Amurka ba su laminta da yadda Joe Biden yake goyon bayan Isra’ila ba.

Sakamakon ra’ayin jama’ar kasar da su ka saurara yana nuni da cewa masu goyon bayan siyasar Biden dangane da yakin Gaza,ba su wuce kaso 1/4 na mutane ba.

Daga fara yakin na Gaza, gwamnatin Joe Biden ta aike da manyan jami’anta zuwa Tel Aviv domin nuna goyon baya na siyasa da soja, sannan kuma ta rika aikewa da dukkanin makaman da take bukatuwa da su a kisan kiyashin da take yi wa Falasdinawan Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments