Faransa Ta Dauki Matakai Masu Tsauri Gabanin Zanga zanga

Rahotanni sun ce an zuba jami'an 'yan sanda da jami'an tsaro kimanin 70,000 a faɗin Faransa, wanda ya dara na makon da ya gabata.

A faransa masu zanga zanga sun shirya fitowa a wnanan Asabar duk da matakai masu tsanani da gwamnatin da hukumomin wasu yankunan kasar suka dauka na dakile zanga zangar a fadin kasar, saboda tsoron sake afkuwar rikici irin na makon da ya gabata.

An haramta zanga-zanga a Lyon, Toulon, Rouen, da Le Mans.

Rahotanni sun ce an zuba jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaro kimanin 70,000 a faɗin Faransa, wanda ya dara na makon da ya gabata da fiye da

10,000.

A birnin Paris, an ba da izinin yin tattaki guda kawai, matakin da kungiyoyi da ke shirya zanga-zangar sukayi yi Allah wadai da shi.

Babbar kungiyar Kwadago ta CGT, ta yi tir da matakin da ta ce na hana ‘yancin yin zanga-zanga ne, hasali ma karan tsaye ne ga dimokuradiyya.

Kungiyar ta yi kira ga ma’aikata da su yi gangami a ranar 5 ga Nuwamba domin nuna fishi ga matsalar wutar lantarki da kuma kin amincewa da karin albashi ga ma’aikata.

Tuni Kungitar ta CGT ta fara tattauna shawarar kan shiga yajin aiki a ranar 5 ga Nuwamba.

“‘Yancin yin zanga-zanga shi ne tushen dimokuradiyya; shi ne abin da ke bambanta dimokuradiyya da mulkin kama-karya,” in ji Sophie Binet sakatariyar kungiyar kwadigo ta CGT a faransa.

Lamura dai sun rincabe a Faransa bayan zanga zangar da aka gudanar a ranar Asabar data gabata wacce ta rikide zuwa tarzoma da artabu tsakanin jam’ian tsaro da masu zanga zangar kan tsadar rayuwa da hauhawan faranashin makamashi da ta samo asali daga boren daliban sakadare dake nuna fishi kan halin ko kula na gwamnatin E Macron kan sha’anin ilimi a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted