Babbar kungiyar kwadigo ta (CGT), a Faransa ta yi kiran wani sabon yakin aiki da zanga-zanga a ranar 17 ga Nuwamba, tana mai Allah wadai da da mafi karancin albashi da gwamnatin kasar ta sanar.
Tunda farko dai gwamnatin kasar ta sanar da kara mafi karancin albashi da kashi 1.6% daga ranar 1 ga Disamba, kwatankwacin Karin Yuro 23 a cikin mafi karancin albashi, a yayin da wasu kungiyoyin ke neman a kara albashin da Yuro 150 a kowane wata cikin gaggawa.
Baya ga kungiyar ta CGT, akwai wasu kungiyoyin da suka hada da UNSA, FSU, Solidaires, CFE-CGC, da FAFP wadanda suka bayyana anniyarsu ta sake fitowa zanga zanga.
Kafin nan dai an shirya cewa kungiyoyin kwadago za su gana da Firaministan kiasar Sébastien Lecornu a fadarsa ta Matignon a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba.
Yau wata guda kenan da kungiyoyin ke gudanar da zanga zanga akasar ta Faransa kan tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi da tabarbarewar sha’anin ilimi a kasar wacce ta samo asalidaga fishi na daliban makarantun sakandare kan halin ko kula da suak ce gwamnatin kasar na nunawa kan harkar daukar karatu a cikin makarantun dama tsarin wucewa zuwa jami’a.